Hakanan Jam’iyyar LP Ke Cewa Tana Da Ƙarfi, Ni Har Yanzu Bansan Ɗan Takarar Gwamna Ba – Gwamnan Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce bai san dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour ba a jihar Nasarawa.
Sule ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels yayi dashi a cikin shirin siyasar mu a yau.
Jam’iyyar Labour Party ta fara yakin neman zaben gida-gida a fadin kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa.
Da aka tambaye shi ko LP na barazana ga jam’iyyar All Progressives Congress a Nasarawa, sai ya ce, “Karfin Labour ya kasance da ita kanta kungiyar kwadago, NUT, NUTRW da sauran su. Don bayanin ku, ba sa cikin taron. Sun fito karara sun amince da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Nasarawa kuma sun bayyana dalilansu don haka ba a gayyace su ba.
“An kuma gayyaci shugabannin kwadago a Jihar Nasarawa su je su gabatar da irin wannan wasan kwaikwayo. Sun hada da takwaran su na jihar Kebbi sun kuma amince da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kebbi saboda abin da suka nuna a jihar Nasarawa.
