INEC Za Ta Ɗauki Ma’aikatan Wucin-Gadi 10,000 A Jami’ar BUK

INEC Za Ta Ɗauki Ma’aikatan Wucin-Gadi 10,000 A Jami’ar BUK

A jiya Laraba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta bayar da foma-fomai dubu goma ga shugaban jami’ar Bayero Kano, Farfesa Sagir Abbas domin daukar ma’aikatan jami’ar na wucin-gadi a zaɓen 2023.

Darakta-Janar na Hukumar ta INEC, Lawal Sauri, wanda ya gabatar da foma-foman, ya ce duk masu sha’awar yin aikin na wucin-gadi a jami’ar za su iya nema domin yin aikin zaɓen na 2023.

Sauri ya bayyana cewa “an bada foma-foman ne ga bangarorin koyar wa da ba na koyar wa ba, da kuma daliban da za su so su shiga aikin zaben.”

Don haka, ya yi kira ga masu sha’awar da su “yi amfani da intanet sannan su zo domin karbar fom din a hannu.”

Sauri, wanda ya samu rakiyar manyan ma’aikatan hukumar, duk da haka, ya jaddada cewa “Wadanda suka nemi yin aikin ta yanar gizo ne kawai za a yi la’akari da su.”

A nasa jawabin jim kadan bayan karɓar foma-foman,Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya yabawa INEC kan daukar BUK a matsayin “abokiyar aiki da ta dace.”

Ya ba da tabbacin cewa “hukumar jami’a za ta raba foma-foman ga duk masu sha’awar kuma za su tabbatar da cewa an dauki wadannan mutane aikin zaben.”

Tuni dai Farfesa Adamu Abbas ya bayar da umarnin a fitar da wata takarda ta sanarwa don yin kira ga masu sha’awar yin aikin da su fito domin karbar fom din

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *