Wata wasiƙa da Babban bankin Nijeriya ya aike wa majalisar ƙasar ta nuna cewa Gwamnan babban bankin Emefiele ba zai samu damar halarta gaban ƴan majalisar tarayya ba kamar yadda suka buƙata.
Gwamnan bankin na CBN dai takardar ta ce ya kamu ne da rashin lafiya shi yasa ba zai samu zuwa ba.
Saidai a cikin takardar an nuna cewa, maimakon shi Emefiele ɗin mataimakiyarsa, Aisha Ahmad zata zo a madadinsa.
