Iyalan wasu jami’an soja da ake tsare da su kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu sun roƙi shugaban ƙasa da rundunar sojin Najeriya su ba su damar ganin ‘yan uwansu tare da tabbatar da an yi musu shari’a a fili kuma cikin adalci kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.
Iyalan sun yi wannan kira ne a wani taron manema labarai a Abuja, inda suka ce jami’an sun shafe sama da kwanaki 160 a tsare, kuma suna fuskantar matsin lamba da kuma yaɗa labarai a kafafen watsa labarai kafin shari’a.
Sun kuma roƙi uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta tausaya musu tare da taimakawa wajen ganin an yi adalci.
Iyalan sun jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi a ɗauki wanda ake zargi a matsayin mara laifi har sai an tabbatar da laifinsa, don haka suka buƙaci a gaggauta fara shari’ar a kotu a bainar jama’a maimakon shari’ar sirri ta soja.
A baya, jami’an tsaro sun ce sun kama mutane kusan 40 da ake zargi da hannu a wani shirin juyin mulki, ciki har da jami’an soja, dan sanda da wasu fararen hula, tare da kwato makamai da motocin aiki da ake zargin an tanada domin aiwatar da shirin.
