Ƙasashen Duniya Sun Yabawa Shugaba Buhari Kan Kyakkyawan Shugabanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin wannan mako, ya lashe zukatan ’yan uwansa shugabannin Afirka a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, inda suka yi ta ba da shaida masu kyau na halayen shugabancinsa.

Shugabannin kasashen Afirka sun je birnin Yamai ne domin halartar taron kolin bunkasa masana’antu da habaka tattalin arzikin kasashen Afirka, da kuma wani zama na musamman kan yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).

Shugabannin kasashen Afirka sun yi amfani da damar taron wajen halartar bikin kaddamar da littafin ‘Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria’, wato kalubalen shugabanci a Najeriya wanda ya gudana a Yamai.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin, shugaba Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijar ya bayyana shugaban na Najeriya a matsayin ”mutumin da ba shi da ra’ayin mazan jiya, mutum ne mai tawali’u, mai kishin kasa kuma mai kishin demokradiyya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *