Ƴan Bindiga Sun Hari Kan Ma’aikatan INEC A Enugu
Akalla mutane biyu ne aka kwantar a asibiti bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an hukumar zabe mai zaman kanta Kaita kasa (INEC) a karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.
Shugaban Hukumar INEC, a sashen Watsa Labarai da Ilimantar da masu Zabe, Festus Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Alhamis.
Ya ce maharan sun lalata na’urar tantance masu kada kuri’a guda biyu a yayin harin
Sanarwar ta bayyana cewa an kai wa jami’an hari ne a yayin da suke ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a (CVR) a wata makarantar firamare da ke Umuopu da ke Umuozzi Ward 19 a jihar Enugu.
Ya ce, “’yan bindigar sun yi ta harbe-harbe ba kakkautawa don tarwatsa masu rajista da jami’an rajista. A rikicin da ya biyo baya, daya daga cikin ma’aikatanmu ya samu raunuka kuma yana karbar magani a asibiti,” in ji sanarwar.
“An yi asarar injunan rajistar masu kada kuri’a guda biyu da kayayyakin ma’aikata kamar wayoyin hannu.
“Saboda haka, an dakatar da rajistar masu kada kuri’a a gundumar a Igboeze North.”
A cewar Okoye, hukumar ta kai rahoton lamarin ga hukumomin ‘yan sanda a jihar Enugu domin fara bincike
