Ƴan Bindiga Sun Kashe Jami’an Ƴan Sanda A Jihar Enugu

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Wasu ƴan bindiga a ranar daren Laraba sun kai hari inda suka kashe jami’an ƴan sanda 3 a Jihar Enugu.

Majiyar Jakadiya ta bada rahoton cewa, lamarin ya a wurin zama na Chime Avenue, na New Haven, dake Ƙaramar Hukumar Enugu ta Arewa a Jihar.

Wata majiyar ta bayyana cewa, ƴan bindigar na tuka motar kirar sienna sun rufarwa motar jami’an sanda ƙirar hilux tare da buɗe mata wuta.

An bayyana cewa jami’an yan sanda ukku ne suka rasa rayukansu a wurin da lamarin ya faru.

Rundunar Ƴan sandan jahar Enugu har yanzu bata bada wata sanarwa ba dangane da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *