Ƴan Sanda Sun Dakatar Da Yunƙurin Fashi A Wani Bakin Abia

Daga Wakiliyar mu Amira Salisu Batsari.

Rundunar Ƴan Sandan Jahar Abia, ta tabbatar da cewa jami’an ta sun tarwatsa yunƙurin gudanar da wani fashin Banki da Ɓarayi suka yi niyyar yiwa Abokanan huldar Banki dake Umuahia, Babban birnin Jahar Abia a ranar Alhamis 14 ga watan Yuli.

A cikin wata sanarwa daga Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Mr Gieffrey Ogbonna, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a library Avenues wadda akafi sani da hanyar Banki.

Ogbonna ya ƙara da cewa, ƴan fashi da makamin sun taɓa kai hari ga Abokanan hulɗar Bankin waɗanda suka je bankin domin fitar da Kuɗaɗe masu yawa.

Ya bayyana cewa, Dabar Ƴan fashin guda uku, da suka buɗe wuta suna cikin wata jar mota ƙirar Toyota-corolla, sun yi arangama da jami’an ƴan sandan dake kula da bankin a cikin gari a wajen cin abinci na Hoeffers dake kan hanyar Factory, Umuahia, a yayinda suka tsaya domin jiran waɗanda suke so su yiwa Fashi.

Ya bayyana cewa, a lokacin da suka ga jami’an masu kai sama me, barayin sun cigaba da harbi ko’ina harbi domin samun hanyar guduwa, inda suka kwaci wata mota domin barin wurin, Wanda shine ya haifar da musayar wuta tsakanin jami’an yan sanda da Yan fashin.

sanarwar tace “abin baƙin ciki a lokacin musayar wutar, harsashin su ya taɓa jikin jami’in Ɗan Sanda , da mutane biyu dake wurin da abun ya faru.

“Anyi saurin Kai wadanda lamarin ya rutsa dasu zuwa Asibitin Kwararru dake Umuahia, a yayin da Akayi nasarar kama mota Mai lamba LND 126 KL, da bindaga ƙirar AK-47 tare da jikkar harsashi guda uku, da Adda guda ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *