Ɗan Majalissar Benue Ya Fice Daga Jam’iyar APC Zuwa PDP

Honarabul Jacob Orban mai wakiltar mazabar Katsina-Ala ta yamma a majalisar dokokin jihar Benue ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Sanarwar Ficewar Orban na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa kakakin majalisar dokokin jihar, Rt Hon Titus Uba kuma mataimakin kakakin majalisar, Rt Hon Christopher Adaji wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar Talata, 26 ga watan Yulin shekarar 2022 ya karanta.

Ya bayyana rashin tsarin tafiyar da dimokuradiyyar a cikin gida a jam’iyyar APC a matsayin babban abin da ya sanar da sauya shekarsa, inda ya ce sabanin da aka samu ya haifar da samuwar bangarori da kungiyoyi da dama a cikin jam’iyyar.

Dan majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin riko na majalisar dokokin jihar Benue mai kula da al’adu da yawon bude ido, ya bayyana jin dadinsa ga shugabanni da mambobin jam’iyyar APC bisa ba shi damar tsayawa takara a karkashin inuwarta

Da yake mayar da martani, mataimakin kakakin majalisar, Rt Hon Christopher Adaji, a madadin ‘yan majalissar ya taya wakilin Katsina Ala Ta Yamma murnar ficewa daga jam’iyyar tsintsiya zuwa jam’iyyar PDP tare da ba shi tabbacin samun dama a sabuwar Jam’iyar.

Ficewar Hon Orban zuwa PDP ya kawo adadin ‘ya’yan PDP a Majalisar Jiha zuwa ashirin da shida a halin yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *