Alhazan Jihar Kwara 541 Sun Koma Gida, Sun Bukaci Riƙa Kulawa Dasu A Ƙasa Mai Tsarki

Alhazan Jihar Kwara 541 Sun Koma Gida, Sun Bukaci Riƙa Kulawa Dasu A Ƙasa Mai Tsarki

Kashi na farko na maniyyata 541 da jami’i ɗaya daga jihar Kwara sun dawo gida bayan kammala aikin hajjin Shekarar 2022.

Daily Trust ta ruwaito cewa maniyyatan da suka ratsa kananan hukumomi 16 na jihar, sun isa filin jirgin sama na Ilorin da karfe 7:59 na safe a cikin jirgin Max Airline mai lamba 5N-ADM a ranar Alhamis.

Wasu daga cikin mahajjatan da suka zanta da Daily Trust sun gode wa Allah da wannan nasara da aka samu, amma sun bukaci hukumomi da su tabbatar da cewa an samu kura-kurai a wannan Hajjin da aka samu an gyara shi.

A cewar ɗaya daga cikin mahajjatan, Alhaji Tunde Kanike, wanda ya godewa Allah da kuma gwamnatin jihar bisa nasarar da suka samu, ya kamata a inganta jindaɗin Alhazai a Hajjin mai zuwa.

Ya ce, “Hukumar Alhazai ta jiha tana buƙatar ta kara inganta harkokin jin dadin alhazai musamman a bangaren abinci na gida.

“Da yawa daga cikinmu ba mu ji daɗin abincin da aka tanadar ba yayin zaman mu a ƙasa Mai Tsarki.”

Alhaja Kuburat Abimbola-Lawal, yayin da take godewa jihar da jami’ai bisa kokarin da suka yi, ta jaddada bukatar gyara kura-kuran da aka samu a lokacin Hajji na bana.

A nasa bangaren, wani mahajjaci da ya gwammace a sakaya sunansa, ya ce tilas ne hukumomi su ba da fifikon muhimmancin aikin da kuma tunkararsa da muhimmanci.

“A inda batun ya fara shine yawancin jami’an da suka tafi tare da mu ƴn farko ne kuma lamarin ya mamaye su.

Har ila yau, babu wani ingantaccen tsarin aiki tsakanin jihar da jami’an NAHCON wanda hakan ya kara mana wahalhalu a al’amura,” inji shi.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar, Misis Jumoke Jimoh, wadda ita ma ta shaida Hajjin, ta shaida wa Daily Trust cewa a mako mai zuwa ne ake sa ran kashi na biyu za su dawo jihar.

Wani faifan bidiyo ya bazu a jihar inda mahajjatan suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da shirin masauki a Saudiyya yayin atisayen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *