Fadar Shugaban Ƙasa Ta Ƙaryata Gudaji Kan Zargin Emefiele Da Karkatar da Tiriliyoyin Nairori
Fadar Shugaban Kasa ta ce sam babu kamshin gaskiya a zarge-zargen da dan majalisa Gudaji Kazaure ya yi wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na karkatar da kudaden da yawansu ya kai Naira tiriliyan 89.1.
Gudaji Kazaure, dan Majalisar Wakilai daga jihar Jigawa a cikin wani bidiyo da ya karade intanet, ya zargi gwamnan na CBN da kokarin yin rufa-rufa kan badakalar kudaden na harajin shigo da kayayyaki daga kasashen waje.
Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa da gangan wasu makusanta Shugaban Kasa suka hana shi ganawa da shi domin kada ya gabatar masa da sakamakon binciken nasa.
Kazalika, Gudaji Kazaure ya yi ikirarin cewa Buharin ne ya nada shi Shugabancin kwamitin domin ya gano badakalar da ke cikin binciken.
To sai dai a cewar Kakakin Buhari, Malam Garba Shehu, sam kwamitin da Gudajin yake ikirari haramtacce ne, kuma tuni Buharin ma ya rushe shi.
