An Gudanar Da Bikin Faretin Karnuka A Legas

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito cewa masu karnuka a birnin Legas da ke kudancin Nijeriya, sun fito don nuna karnunkansu a wani bikin nuna dabbobi karo na hudu da aka yi a karshen makon da ya wuce a jihar.

Karnukan da aka zo su wajen sun fito cikin kwalliya bayan an sanya musu kaya masu kyau.

Manufar bikin ita ce don a fito a nuna cewa ba gaskiya ba ne cewa ‘yan Afirka na gallaza wa karnukansu.

Wadda ta shirya bikin Jackie Idimogu, ta ce ” Mun shirya bikin ne don mu fahimtar da mutane cewa karnuka ba wai gadi suke mana ba kawai, a kodayaushe muna tare da su”.

Karya Pasha, wacce ta sanya kaya iri daya da mai ita ta sha gilashi kuma ita ce karyar da ta lashe kyautar bana a wajen bikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *