Ina Da Lafiya Da Ƙarfin Da Zan Jagoranci Najeriya – Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da goyon bayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana da kwarin gwiwar zai jagoranci kasar nan.

Da yake jawabi a wajen taron tattalin arziki da zuba jari na Kaduna karo na 7 a ranar Juma’a, Tinubu ya roki El-Rufai da ya dawo kasar nan a 2023 domin ya yi aiki tare da shi idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Ya ce, “Idan ka bar ni a kan mumbari, zan ci gaba da yakin neman zabe a nan, ina rokon El-Rufai da kada ya gudu daga Najeriya a 2023 saboda muna bukatar kirkirar ka a wannan mawuyacin lokaci.

“Ina gaya muku da kwarin gwiwa cewa zan jagoranci kasar nan a 2023 tare da goyon bayanku. Ina da ikon shawo kan dukkan matsalolin da kuma kawo kasar kan turbar ci gaba.”

Dangane da rashin tsaro, Tinubu ya ce, “Ba wani inci na kasar nan da za a amince da ‘yan fashi da makami, za mu yi yaki da su. A karkashin jagorancina, za mu yi amfani da fasahar yaki da tada kayar baya wajen kawar da miyagun laifuka a cikin al’ummarmu kuma rayuwarku za ta kasance cikin kwanciyar hankali.”

Da yake magana kan tattalin arziki, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ce, “Za mu mayar da saukin yin kasuwanci a kamfanoni da kuma tabbatar da samar da wutar lantarki da rarraba wutar lantarki a kai a kai.

Ya ci gaba da cewa Najeriya za ta yi nasara kuma za ta ci gaba da samun wadata inda ya ce, “Zan tattaro hazikan ‘yan Najeriya maza da mata domin ci gaban kasarmu. Za mu yi amfani da gwamnatin da ta dace da za ta toshe alkaluman kudaden shiga don yin lissafin da ya dace.”

Da yake mayar da martani, El-Rufai ya yi alkawarin ci gaba da zama a kasar ko da kuwa na wucin gadi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *