Jami’ar Bayero ta sha alwashin binciken kan zargin wani ɗalibi da ya damfari Farooq Kperogi kuɗi da sunan neman taimako

Hukumar gudanarwar jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta ce ta fara bincike kan zargin da ake wa ɗalibanta da yin basaja da damfarar kuɗi ta amfani da intanet.

Mai magana da yawun jami’ar, Lamara Garba, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba biyo bayan iƙirarin da wani ɗan Najeriya mazaunin Amurka, Farooq Kperogi, ya yi.

Kperogi ya yi zargin cewa Ismail Sani wanda ɗalibi ne da ke shekara ta 3 (300-level) kuma yana ɓangaren koyar da likitanci na daddabobi (Veterinary Medicine) a BUK. Dalibin dai yana basaja ne a intanet tare da neman taimako daga wajen mutane.

A cikin jawabin, Garba ya ce jami’an ta fara bincike a matakin farko na tabbatar da gaskiyar zargin da kuma gano ɗalibin kansa.

“Hukumar jami’ar na tabbatar da cewa jami’ar Bayero Kano ba ta wasa da maganar ɗa’a da kyakkyawan halayya ga ɗalibai a lokacin da suke karatu,” in ji jawabin.

“Jami’ar nan ba za ta lamunci duk wani abu da zai ɓata sunanta ba.”

Garba ya ce tanadin ladabtarwa na jami’ar ya shafi ɗalibai ne kaɗai ba tsofaffin ɗlibai ba.

Sakamakon zargin da ake, jami’a ta fara bincike domin tabbatar da gaskiyar wannan zargi,” ya bayyana. “Za a ɗauki matakin da ya dace a yayin da jami’a ke bin matakanta na ɗa’a da tafi da ɗaliban jami’ar.”

Jami’ar ta kuma ce abin da ake zargin ɗalibin da aikatawa kwata-kwata ba koyarwar jami’ar ba ne.
Daga nan ne BUK ta yaba mutanen da suke taimaka wa ɗalibai da kuɗi, yana mai cewa irin wannan taimako na taiamaka musu wajen samun ilimi.

Ya ba da tabbacin da zarar an tabbatar da zargin da ake wa ɗalibin, jami’a za ta ɗauki matakin ladabtarwa daidai da tanadin doka.

Game da zargin da Kperogi ya yi:

Kperogi ya ce da farko Sani ya yi basaja ne a matsayin ɗaliba mace da sunan “Halima Tahir” domin neman taimako na kuɗi.

A cewar lakcaran da ke koyarwa a jami’ar Amurka, ɗalibin ya yi masa magana ne a farkon watan Satumbar 2024 inda ya ce shi ɗalibi ne da ke neman taimakon biyan kuɗin makaranta bayan samun gurbin karatu a sashen koyar da likitancin kula da dabbobi a BUK.

Kperogi ya ce, ya taimaka masa da kuɗi kuma daga baya ya samu ƙarin neman taimako na kuɗi da ya haɗa da neman ya taimaka wajen siya wa wata dattijuwa magani.

Ya ce, wannan ɗalibin ya sake biyo shi, amma da sunan “Halima Tahir” domin ya taimaka masa da kudi.

“Bayan gudanar da bincike da na yi, na gano cewa ‘Halima Tahir’ wani ne mai suna Ismail Sani,” in ji Kperogi.

Ya ce, binciken imel da takardun biyan kuɗi da lambar waya duk sun nuna cewa na Sani ɗan damfara.

Kperogi ya kuma yi ikirarin cewa wanda ake zargin ya musanta aikata kuskuren duk da tarin hujjoji masu yawa.

“Na bayyana masa hujjoji kuma a shirye nake na yafe masa idan ya nemi gafara kuma ya yarda ya sauya halinsa,” ya rubuta. “Sai dai ya ƙi yarda har da ransuwa da Allah.”

Malamin jami’ar ya ci gaba da cewa akwai mutane da dama da shi dai ɗalibin ya yi wa irin abin da ya yi min.

“Ina da tabbacin akwai mutane da dama da ya damfara da ban ko su wane ne ba,” ya faɗa.
Kperogi ya ce, ya wallafa bayanan ne domin mahukunta jami’ar Bayero su gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *