Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar tabbatar da ingantaccen mulkin dimokuraɗiyya tare da girmama doka da oda a Najeriya.
Yilwatda ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, inda ya ce Shugaba Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen kare tsarin dimokuraɗiyya da bin dokokin ƙasa, musamman bayan da ya sanya hannu kan Dokar Zaɓe ta shekarar 2026.
Shugaban APC na ƙasa ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, bayan halartar wani taron buɗe baki na mabambantan addinai (Musulmi da Kirista) da aka gudanar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.
A taron akwai Shugaban ƙasa, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, shugabannin jam’iyyar APC da kuma mambobin Inter-Party Advisory Council (IPAC).
A cewar Yilwatda, taron ya nuna irin haɗin kai da ke tsakanin shugabannin siyasa da na addinai, tare da jaddada aniyar su ta bai ɗaya wajen tabbatar da ci gaban Najeriya.
Ya ƙara da cewa bambancin al’adu da addinai da ke tsakanin al’ummomin Najeriya ya kamata a duba shi a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin kai, maimakon ya zama abin da zai raba kan jama’a.
Yilwatda ya ce ya kuma yi amfani da damar wajen yabon Shugaba Tinubu bisa irin hidimarsa ga ƙasa, tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga manufofi da alkiblar gwamnatin sa.
A ƙarshe, ya bayyana cewa taron buɗe bakin na mabambantan addinai ya sake jaddada muhimmancin haɗin kai da shugabanci na bai ɗaya domin ƙarfafa tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.
