Jami’an tsaro a Jihar Zamfara sun kama wani matashi da ake zargi yana jigilar harsasai 800 na bindigar AK-47, wadanda ya boye a cikin tankin man babur kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin, mai suna Mannir Adam mai shekaru 25, da misalin karfe 7:50 na yammacin ranar Talata a kan hanyar Gusau zuwa Funtua.
A cewar wata majiya ta bangaren tsaro da ta zanta da Zagazola Makama, wani shafin yada labarai da ke mayar da hankali kan rahotannin yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, an cafke Mannir ne a wani wurin duba ababen hawa na jami’an tsaro da ke Yankara.
Rahotanni sun ce Mannir Adam, wanda mazaunin ƙauyen Yankuzo ne a ƙaramar hukumar Tsafe, yana tukin babur mai launin ja nau’in “Boxer” lokacin da jami’an tsaro suka tare shi tare da gano harsasan da ya boye a cikin tankin man babur din.
Majiyoyin tsaro sun bayyana wannan kama a matsayin wata “babbar nasara” a kokarin da hukumomi ke yi na dakile shigo da makamai da harsasai zuwa hannun kungiyoyin masu laifi da ke addabar al’ummomi a Zamfara da wasu jihohi makwabta.
