Rahotanni sun bayyana cewa matashin ana zarginsa da satar wasu muhimman kayan dakin gwaje-gwaje, ciki har da microscope, daga wani dakin gwaje-gwaje na makaranta dake birnin Dutse.
Jami’an NSCDC sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike kan bacewar kayan, wanda daga bisani ya kai ga gano shi.
Hukumar ta kara da cewa bincike na ci gaba domin gano ko akwai wasu da suka hada baki da shi wajen aikata wannan laifi.
