Yadda Ɗan bindiga Ya Hallaka Ƙawar Fira Ministar Italiya A Wajen Chashewa
Wani mutum ya kutsa kai cikin wata mashaya a gundumar Fidene, Rome, babban birnin Italiya, ya bindige wasu mata uku har lahira ciki har da wata kawar firaministar Italiya Giorgia Meloni a jiya Lahadi.
Wasu mutane hudu kuma sun jikkata sakamakon harbin da aka yi a lokacin da su ke cikin wani taro a matsayin wani bangare na kwamitin mazauna yankin, kamar yadda BBC ya ruwaito.
Magajin garin Rome, Roberto Gualtieri ya bayyana harbin a matsayin “babban tashin hankali” kuma ya ce zai kira taron gaggawa kan lamarin.
Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin mai shekaru 57, Claudio Campi tare da tsare shi.
Rahoton ya bayyana cewa Campi ya kasance cikin jerin gwano tare da wasu daga cikin shugabannin kwamitin.
Luciana Ciorba, mataimakiyar shugaban kwamitin, wacce ke wurin da abin ya faru ta ce dan bindigar ya shiga mashayar ya yi ihu, “Zan kashe ku duka” kafin ya yi amfani da bindigarsa.
Rahotanni sun ce wasu ne a wajen da abin ya faru suka rinjayi maharbin kafin ‘yan sanda su tsare shi.
Daga cikin mutanen da suka jikkata, wadanda ake kyautata zaton mata biyu ne da maza biyu, daya na cikin mawuyacin hali.
