Goodluck Ga Matasa: Ku Jefar Da Ƙabilanci, Addini, Ɓangaren Ci Wajen Zaɓen Shuwagabanni

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci matasa da su yi watsi da masu kokarin raba kasar da siyasar kabilanci da addini gabanin zaben 2023.

Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Owerri a wajen taron cika shekaru 80 na Cif Emmanuel Iwuanyanwu.

Jonathan ya lura cewa siyasar Najeriya ta kunno kai cikin kabilanci da addini “don cutar da kasarmu da kuma tushenmu. Ina ganin ya kamata mu rage wannan.”

“A dunkule, idan muka hada kai muka daidaita sabanin dake tsakaninmu, za mu iya gina kasa da kowa zai san nasa. Kuma za a tabbatar da hakkin kowa.

“Hakan ya kamata mu bi – Najeriya inda adalci, gaskiya da daidaito ke mulki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *