Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Asabar din nan ya gana da ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar daga sassan kasar nan.
Tsohon mataimakin shugaban kasar tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, sun gana da ‘yan takarar a gidansa da ke Asokoro, da ke Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da ‘yan takarar gwamna daga jihohin Kaduna, Plateau, Katsina, Lagos, Niger, Kano, Sokoto, Delta, Yobe, Jigawa, Nasarawa, Kwara, Benue, Borno, Ebonyi da Zamfara.
Gidan talabijin na Channels ta rawaito cewa, An gudanar da taron ne a sirri gida.
