Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Nanah Opiah, ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin tarayya ta tsaya kan tsarin babu aiki, babu biyan albashi ga malaman jami’o’i ASUU.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in, ASUU, tuni tayi Allah wadai da wannan tsarin na gwamnatin tarayyar.
Ministan, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ta hannun mai taimaka masa kan kafafen yada labarai, Kelechi Mejuobi, ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance rikicin, dake tsakaninta da ASUU.
Opiah, wanda ya kai ziyarar aiki a Jami’ar Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, yayin da yake nadamar yadda yajin aikin ya jawo koma baya a fannin ilimi inda gwamnati, dalibai, iyaye, da malamai suka yi asara, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su sanya baki.
Ya kuma yi kira ga shugabannin majalissar gudanarwar jami’o’i da su shigo cikin lamarin su shawo kan ASUU ta sake duba matsayarta.
