Mamakon Ruwa Ya Haddasa Ambaliyar Ruwa A Warawa Ta Kano

Mamakon ruwan sama ya haddasa rushewar gidaje a wasu kauyuka dake yankin Ƙaramar Hukumar Warawa.

Yanzu haka dai wasu al’ummar yankin da abin ya shafa suna gudun tsira da rayuwarsu, sakamakin ambaliyar ruwan, wadda ta afku sakamakon ruwan saman.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa akwai wasu da dama wadanda suka fake a makarantu da masallatai.

Wani mazaunin yankin Malam Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya alakanta faruwar lamarin da matsalar magudanan ruwa.

Duk kokarin ji daga bakin shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA, abun ya ci tura.

Tun daga Asubahin jiya ake ci gaba da shan ruwan Sama a jihar Kano, har kawo wannan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *