Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa ta kama wata mai suna Alice Mulak akan laifin dabawa saurayinta wuka inda tayi sanadiyyar mutuwar a karamar hukumar Karu dake a jihar.
Wannan na kunshe ne acikin wata takarda da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda jihar DSP Ramhan Nansel ya rabawa wakilinmu ranar juma a babban birnin jihar wato Lafia.
A cewar takardar, jami’an yan sanda yankin Mararaba ‘A’ dake jihar Nasarawa a karkashin jagoranci kwamishinan Yan sandan jihar Musa Babayola sun kama wata budurwa mai suna Alice Mulak a unguwar Gwari dake a karamar hukumar Karu da laifin dabawa saurayinta wuka inda ta kashe har lahira.
” Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru kusa da gidan shakatawa na City Rock dake Mararaba da misalin karfe ukku da rabi yayin da mamacin da budurwar tashi suka fara faɗa har ta kai ga kai ma juna bugu sakamakon rashin fahimtar da suka samu
” Yanzu haka an kama wace ake zargin tare da wukar da tayi amfani da ita wurin aikata kisan a bisa umarnin kwamishinan yan sanda CP Adesina Soyemi.”
Nensel ya kuma kara da cewa an mayar da wace ake zargin a cibiyar sashen binkiciken masu aikata munanan laifuka domin kara bincike dangane da lamarin.
