Shigabannin ƴan ta’adda da dama a Katsina a jahar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya sun aje makamansu da roƙon gwamnatin jahar da ta duba yiwuwar yin wani sasancin da su.
Mai bai wa Gwamna Masari shawara kan harkokin tsaro Ibrahim Katsina ne ya faɗi haka a yayin wata fira da ya yi da gidan talabijin na channels a ranar Friday ɗin da ta gabata.
Ya ce shugabannin ƴan bindigar sun fahimci aikace-aikacen ta’addaci ba abu ba ne da zai haifar da ɗa mai ido a gare su zuwa gaba saboda haka suka roƙi gwamnatin da ta yafe masu a sake wani sasancin.
Katsina ya ci gaba da cewa irin salo da ƙwarewa wajen ɓullo da dabarun kare ƴan jahar da kuma tunkarar ƴan ta’addar gadan-gadan ya sanya a samu zaman lafiya ba kamar da ba.
Ya ce yana da tabbacin cewa nan da ɗan lokaci kaɗan aikace-aikacen ƴan ta’addan zai zama tarihi duba da yadda ake samun haɗin kai daga jama’a wajen bada sahihan bayanai ga jami’an tsaro.
Daga ƙarshe ya buga misali da yadda gwamnatin jahar ta horar da mutane masu ilimi sosai har su 1,100 a matsayin yan banga da suka yarda su bada gudunmawarsu wajen yaƙi da ta’addacin da kuma kira da gargaɗin ƴan bindigar akan su aje makamansu domin a zauna lafiya
