Yanzu Lokaci Ne Da Arewa Za Ta Saka Maka Alherin Da Ka Daɗe Kana Shuka Mata – Badaru Ga Tinubu
Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ce yankin Arewacin kasar nan zai biya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamna Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Tinubu a Kano ranar Lahadi.
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC , Ahmed Bola Tinubu, ya ziyarci jihar Kano domin bude ofisoshin yakin neman zabensa.
Gwamnonin jihohin Kano, Jigawa da Zamfara ne suka tarbe Tinubu a ranar Asabar a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano tare da dubban magoya bayansa.
Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka hallara, Gwamna Muhammad Badaru ya ce Tinibu ne kadai ya goyi bayan ‘yan takarar shugaban kasa biyar na Arewa.
