Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya NCDC ta ce an samu rahoton ɓullar cutar kwalara da suka hada da mutuwar mutane 256 a jihohi 31 a bana.
NCDC, a rahotonta na jiya, ta ce tsakanin 5 ga Satumba zuwa 2 ga Oktoba, kasar ta sami rahoton mutane 4,153 da ake zargi da kamuwa da cutar tare da mutuwar Mutane 80.
Rahoton ya zayyana jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ekiti, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Lagos, Nasarawa. , Niger, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe and Zamfara.
Ta ce daga cikin wadanda ake zargi da kamuwa tun farkon shekarar, sun kasance masu shekaru 5-14 ne suka fi fama da matsalar, ta kara da cewa daga cikin wadanda ake zargi, kashi 48 cikin dari maza ne.
