Babu Wanda Ya Yaudare Ku, Gbajabiamila Bai Yi Alƙawarin Biyan Ku Albashi Ba – Majalisa Ga ASUU
Majalisar wakilai ta mayar da martani kan zargin da shugaban kungiyar malaman jami’o’in taKasa ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi na cewa shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ya yaudari kungiyar nhar ta janye yajin aikin.
Kakakin majalisar, Ben Kalu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce shugaban majalisar bai taba yi wa malaman alkawarin biyan basussuka ba.
Idan dai za a iya tunawa dai, shiga tsakani da majalisar ta yi ne ya sa malaman suka janye yajin aikin na watanni takwas.
Bugu da kari, kotun da’ar Ma’aikata ta kasa ta umarci ASUU da ta dakatar da yajin aikin. Sannan kuma gwamnati ta dage kan tsarin ba aiki ba biyan albashi.
Farfesa Osodeke, a wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, ya ce Gbajabiamila ya gaza cika yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar.
Da yake mayar da martani kan zargin, Kalu ya ce ko kadan shugaban majalisar wakilai bai yi alkawarin biyan basussukan albashin da ‘yan kungiyar suke bi na tsawon lokacin da suke yajin aiki ba.
Ya ce alkawuran da majalisar ta yi na nuni ne a cikin kudirin kasafin kudi na shekarar 2023, wanda ya hada da Naira biliyan 170 don samar da wani mataki na karin girma a cikin shirin jin dadin malaman jami’o’i da karin Naira biliyan 300 na kudaden farfado da su.
Don haka, Kalu, ya zargi shugaban ASUU da “rashin fahimtar tattaunawa”, ya kara da cewa “dangantakarsa da siyasantar da al’amura, wasu muhimman dalilai ne da jami’o’in suka shiga yajin aiki na tsawon lokaci.”
