Daga Amira Salisu Batsari.
Ministan Ilimi Adamu Adamu ya bayyana cewa matsala guda ɗaya, da ta hana shawo kan Yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya da suke cigaba da yi, shine batun Dokar “Babu aiki Babu albashi”.
Adamu ya bayyana hakan ne a ranar talata ga Manema Labarai a lokacin wani taron da yayi da, Shuwagabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya wanda ya wakana a Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya a Abuja.
“Mu gayawa juna gaskiya dama dukkanin Ƙungiyoyi, musamman ASUU, abu guda ɗaya da Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyoyi ba zamu cimmawa yarjejeniya cikin sauƙi ba, shine batun Dokar “Babu Aiki, Babu Biyan Albashi”. Maganar gaskiya, Gwamnati ta sanar da cewa ba zata iya karya ta ba,” Inji shi.
Ya bayyana godiyarsa ga dukkanin Ƙungiyoyi da sadaukar da kansu na fahimtar matsayar Gwamnati akan wannan lamari.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta kasance cikin wata sabuwar rashin jituwa da Gwamnatin Tarayya sama da watanni shidda wanda ya haddasa rufe kafatanin Jami’oi a Najeriya.
