Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce dan takarar shugaban kasa na APC Asiwaju Bola Tinubu Wanda aka ɓoye rashin lafiyar sa, bai kamata a ɗauke shi da wani Mahimmanci ba.
Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya yi wannan jawabin domin mayar da martani kan kalaman da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu ya yi wa maigidan nasa a wani taron tattaunawa da ‘yan kungiyar Tijjaniyyah a Kano a karshen makon da ya gabata.
Tinubu a lokacin da yake shagube ga Atiku Abubakar, ya ce ba zai zama shugaban kasa na wucin gadi ba wanda zai raba lokacinsa tsakanin Dubai da Najeriya.
Dan takarar na PDP ya shafe mafi yawan lokutan sa a Dubai bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben 2019.
‘
Ibe, wanda ya ce bai kamata a dauki kalaman Tinubu da muhimmanci ba, ya ce: “Shugaban Najeriya, kasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar bakar fata ba ta ƴan wasan barkwanci bace ba,” in ji shi.
“Tsarin zaben shugaban kasa ba jam’iyya ba ce don haka tun da farko APC ta hada gidanta ta fara da kafa kansila. Bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba saboda rashin iyawarsu.
