Gwamnan babban banki Nijeriya CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa, sabbin takardun kuɗin ƙasar tuni sun riga sun isa sauran bankuna a faɗin ƙasar tare da tsammanin cewa bankunan zasu fara amfani da su ga jama’a
Emefiele ya faɗi haka ne a ranar Alhamis ɗin nan jim kaɗan bayan ya fito daga ziyarar da ya kai ma shugaba Buhari a gidansa da ke mahaifarsa ta Daura, a jahar Katsina.
Lokacin da ya ke magantawa da game game da tsokacin da ƴan majalisar taddawa da kuma talakawa su ke yi a kan sabon tsarin kayyade cire kuɗi ya ce an yi tsarin ne ba don a musguna ma kowa ba.
Ya ce wannan tsarin hanya ce mai kyau da zata ƙara inganta tattalin arziƙin ƙasar don haka ba gudu ba ja da baya.
Hakazalika ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su rungumi sabon tsarin da hannu bibiyu tare da bada tabbacin yin duk mai yiwuwa wajen ganin komai ya tafi daidai.
