Tinubu Mutum Ne Mai Tausayi Da I’mani

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ce yana kira ga Atiku Abubakar da Piter Obi da su zo a hada kai domin yi wa kasa da al’umma aiki.

Mataimakin shugaban kasar na magana ne jim kadan bayan hukunci da kotu ta yi kan karar da Atiku da Obi suka shigar bisa zargin yin murdiyar zabe da jam’iyyar APC ta yi a zaben da ya gabata na 2023, inda kotun ta tabbatar da nasarar Tinubu da Kashim.

Ya ce yanzu lokacin siyasa ya wuce lokaci ne da za a hadu domin yiwa yan kasa aiki.

Ya Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mutum ne mai kyakykyawar niya da tausayi da i’mani.

Shettima, ya ce yanzu dai batun hayaniyar shari’a ya wuce don haka zasu yi iya yinsu suka sun share hawayen jama’a.

Ya ce suna sane da cewa, sun san al’umma na cikin mawuyacin hali, amma a yi hakuri suna da kudirin ceto rayuwar jama’a.

Ya ce halin da ake ciki ba da gangan aka shiga ba, ya ce nan ba da dadewa ba za a share hawayen yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *