Wata Mata Zata Sake Yi Wa Mijinta Kaciya
Wata matar aure da ke zama a jihar Kano da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya, ta kudirta cewa zata sake yi wa mijinta kaciya.
A wani labari da kafar sadarwar DCL Hausa ta wallafa, ta bayyana cewa lamarin ne ya sanya mijin matar garzayawa kotu domin neman dauki.
Mijin ikirarin matar ta sa na sake mata kaciya yana hana shi barci idan yana dakinta saboda tsoron kada ta yi masa danyen aiki.
An sha dai samun makamantan wadan nan matsalolin inda wasu mata ke yanke azzakarin al’aurar mazanau saboda tsananin kishi.
