Bola Na Haddasa Hadurran Ababen Hawa A Titunan Katsina

*Rahoto: Ismail Abba*

Kimanin watanni hudu kenan rabon da a ga ana aikin kwashe bola a cikin kwaryar birnin jihar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Lamarin da mazauna cikin birnin ke kokawa game da shi tare da bayyana irin yadda bolar ta mayar da garin kazamin gari da ma haddasa wasu matsaloli masu yawa ga al’umma.

Jakadiya ta zagaya cikin birnin inda ta ziyarci wasu tituna da unguwanni domin gane wa idanu yadda sharar ta takura jama’a kuma daga cikin abubuwan da muka gani sun hada da yadda a wasu unguwannin bolar ta sauka saman titi har ta kai ga masu ababen hawa ba su iya hango wanda ya taho.

Wuraren da muka ziyarta sun hada, unguwar Lay-out da Sabuwar unguwar Kofar kaura, bakin kwabron dorawa da sabon layi, layin da za a bi a je gidansu tsohon gwamna Ibrahim Shema da shararrar fayib wajen farin Masallaci da titin Kofar Marusa da unguwar tayoyi kusa da tankin ruwa da bayan makarantar ATC da dai sauran wurare da ke nuna kusan ko ina haka ake fama da bola a cikin birnin na Katsina.

A zantawar da muka yi da mazauna yankunan, sun bayyana halin da rashin kwashe bolar yake haifarwa gare su da sauran jama’a.

Mubarak Rabi’u a unguwar Layout, ya ce bolar na damun su matuka, ga wari da sauro gami da takura masu ababen hawa da masu tafiya kasa saboda yadda ta gangara saman titi.

Ya ce an daina zuwa a kwashe sai dai suga an zo an kunna ma ta wuta kuma hayakinta na takura mazauna wajen.

Shima wani dattijo da muka zanta da shi a unguwar Sabuwar unguwa, Kwabron dorawa mai suna malam Salisu, ya ce har mushe ake zowa a yada a wurin ga sauro ga kuma hadarurrukan ababen hawa da bolar ke haddasawa.

Shi ma ya ce, rabon da suga anzo a kwashe bolar an kai kimanin watanni hudu yanzu.

A unguwar sabon layi kuwa, bolar ta taru ta tunbatsa har ta kai ga rufe titi guda yadda motoci ba su iya wucewa ta hanyar, nan ma mun samu jin ta bakin wani da ke sana’a a wurin mai suna Umar VC, ya ce lokacin da babu bolar motoci lafiya lau su ke wuce wa amma yanzu mai mashin ma sai da dabara sannan zai iya wucewa.

Akwai matsaloli masu tarin yawa da al’umma ke fuskanta a dalilin bola.

Kadan daga ciki sun hada da fuskantar barkewar annobar amai da gudawa, da zazzabin cizon sauro da haddasa ambaliyar ruwa da shakar gurbataccen iska tare da haddasa hadarin ababen hawa da sauran cututtuka masu hadari ga rayuwar jama’a.

Yanzu haka dai sabuwar gwamnatin jihar Katsina karkashin jagoranci Dr. Dikko Umar Raɗɗa, na gab da cika kwanaki 100 saman karagar mulki kuma yan jihar zasu zura idanu domin ganin ko kwalliya zata biya kudin sabulu a bangaren sha’anin kiyaye muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *