Matsalolin Da Yan Najeriya Ke Fuskanta Ba Laifin Tinubu Ba Ne – Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi II ya ce halin matsin rayuwa da al’ummar Najeriya ke fama da shi a yanzu ba laifin gwamnatin ba laifin shugaba Tinubu ba ne.

Sarkin ya ce, mutane ta ta yi masa tsegwami aka ya kamata ya yi magana amma ya yi shiru da bakinsa ya ki magana.

Sanusi a cikin wani hoton bidiyo da ke yawo saman shafukan sada zumunta, ya bayyana cewa a me ake son ya ce a yanzu tunda a baya sai da ya sha nanatawa cewa za a sha wahala saboda yanayin yadda aka dauko tafiyar da tattalin arzikin Kasar a gwamnatin baya.

“To ni me zan ce? Shekara nawa Ina gaya wa mutane cewa wannan wahalar na gabanmu, in dai an yi min adalci. Sanda aka dauko wannan hanya ta tafiyar da tattalin arzikin Kasa, na fada ba sau daya ba ba sau biyu ba cewa duk wanda ya yi ilimin tattalin arzikin Kasa ya san karshen wannan hanyar wahala za a sha.” Inji shi.

Ya Ci gaba da cewa, ” Kuma na fama na ce wahalar da ake akai kwanaki baya kuma yanzu ma wahalar da ake ciki yanzu ta gaba ta fita wahala”.

Sarki Sanusi, ya huga misali da cewa ire-iren wadan nan abuwa sun faru a Jamani da Zumbabuwe da wasu kasashen ya ce shi ne ya haddasa yakin duniya na 2.

Ya ce yadda aka dauko tsarin tattalin arzikin Kasa a waccen gwamnatin da ta gabata kuma akai ta fada a gyara amma ba a saurare su ba bare a gyara.

Ya ce a wancan lokacin da ya ke cewa a gyara su masu maganar ya fito ya yi magana yanzu ai suka tai suka rinka yi suna cewa shi dan siyasa ne, baya son gwamnati baya son shugaban kasa, ya ce to yanzu kuma ace ya yi magana ya ce me?.

Ya ce shi yanzu iyakarsa ya yi addu’a ya ce Allah ya sawake, ya kuma taimaka wa wadanda ya ke iya taimaka ma wa.

Ya ce shekaru 8 akai ana rayuwa ta karya a gwamnatin baya, komai da aka yi da bashi aka yi shi, ya ce dole ne tattalin arzikin kasa ya durkushe.

Basaraken ya ci gaba da cewa yanzu dai wannan matsalar da ake ciki ba laifin Tinubu ba ne, don haka duk wanda ya soki wannan gwamnatin bai yi mata adalci ba.

Sai dai ya bayyana cewa shi bai ce Tinubu bai laifi ba amma dai a wanna ba laifinsa ba ne, don haka a jira lokacin da zai yi magana zai yi in an zo inda zai maganar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *