Wani jigo a jam’iyyar PDP ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, zai samu kashi 65 na kuri’un jihar Benuwe.
Mista Abraham Chila, wanda mai fafutuka ne na jama’a ya bayyana wannan harsashe yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin nan a Abuja.
Ya ce duk da goyon bayan Gwamna Samuel Ortom ga takwaransa na Ribas, Gwamna Nyesom Wike, a rigimar mulki a PDP, Atiku zai samu kashi 65 na kuri’un jihar.
Ortom ya ce idan har ba a amince da Wike ba, PDP za ta yi kasadar rasa kuri’un jihar a zaben shugaban kasa na 2023.
Chila ya ce ko da wane irin mataki Ortom zai dauka, a lokacin babban zaben badi, PDP da Atiku za su ci zabe a jihar.
Ya ce daga 1999 zuwa yau PDP ta yi karfi a Benuwai.
Ya kara da cewa, kasancewar shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu dan jihar Binuwai ne, ya sa ya zama wajibi babu wani abu da zai iya sauya salon zabe a jihar.
“Ina so ku sani cewa gwamna na, Ortom, shi ma dan takarar kujerar Sanata ne a zaben badi. Wani abin sha’awa shi ne, zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya zai zo a rana ɗaya.
