Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Mutane takwas sun rasa rayukansu, yayin da Mutane biyu suka jikkata sakamakon wani hatsarin mota daya afku a ranar Asabar a Filato.
Jami’in Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Kula da Lare Haɗurra ta kasa reshen jihar Filato, Peter Longsan ya tabbatar da mutuwar mutanen ga majiyar Jakadiya a garin Jos ranar Lahadi.
A cewar sa, hatsarin ya faru da misalin karfe ukku da mintuna goma na ranar Asabar akan hanyar Jos zuwa Lamingo.
Longsan ya bayyana cewa ” hatsarin ya rutsa da Motoci guda biyu motar haya ƙirar Toyota da kuma wata mota Jeep kirar Honda. Mutane 10 ne hatsarin ya rutsa dasu, daga ciki Mutane 8 sun mutu(Manyan Mutane uku maza, da Mata 4, da kuma karamin yaro) a yayinda mutane biyu suka ji raunuka.
“Waɗanda suka ji raunikan an kaisu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, wanda Jami’an ceto na Hukumar Kare Haɗurra suka yi, a yayinda Matattun aka kaisu wurin ajiye gawa na JUTH.
” Hatsarin dai ya faru sanadiyyar mugun gudun da daya daga cikin direbobin keyi wanda ya rasa dakatar da motar harya afkawa motocin guda biyu.”
Jami’in Wayar da kan jama’a na hukumar ya bada shawara ga masu Motoci dasu guji mugun gudu, inda ya bayyana cewa mugun gudu yana haifar da mace- mace da munanan raunika duk lokacin da akayi hatsari.
