Shugabancin Najeriya Na Buƙatar Kaifin Basira Fiye Da ƙarfin Jiki – Inji Tinubu

Bola Tinubu ya yi watsi da cecekucen Jama’a ke yi game da lafiyar sa, yana mai cewa aikin shugaban ƙasa na buƙatar kaifin hankali ne fiye da ƙarfin jiki.

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Alhaji Bola Tinubu, ya sunkuya a lokacin da yake ganawa da mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, lamarin da ka iya ƙara nuna rashin lafiyarsa.

Tinubu dai ya je Gombe ne domin halartar Ɗaurin auren Misbahu Inuwa Yahaya, dan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, daga nan sai ya tsaya don yin wata ziyarar siyasa a fadar Sarkin tare da rakiyar jiga-jigan siyasa da suka haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa Mr. Ahmed Lawan da Sakataren Majalisar Tarayya Boss
Mustapha.

Wasu majiyoyi a tafiyar sun shaidawa Peoples Gazette cewa, Mista Tinubu da Tawagarsa sun je fadar ne domin neman goyon bayan manyan sarakunan Arewa don neman Shugaban kasa a shekarar 2023.

Yayin da aka fara taron an gano Mista Tinubu yana barci yayin da Mista Lawan ke riƙe da makirufo yana jawabi ga mahalarta a falon sarkin.

Har yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya sa Mista Tinubu ya sunkuya a lokacin ziyarar ba, amma ana ta cece-kuce a shafukan sada zumunta game da wannan lamari, inda masu suka su kace hakan ya nuna wani raunin nasa ne, yayin da magoya bayansa kuwa su kace yana yin nazari ne.

Mai magana da yawun yakin neman zaɓen Mista Tinubu bai yi gaggawar mayar da martani akan lamarin ba, wanda ya zo ne a daidai lokacin da ƴan adawa ke ƙara zafafa iƙirarin cewa Ɗan Takarar Shugaban Ƙasar na jam’iyya mai mulki na fama da matsalolin lafiya.

A Ƴan kwanakin da suka gabata ne dai aka ga Mista Tinubu yana yin kalamai da ba su dace ba ko kuma yayi ƙoƙarin kifewa a bainar Jama’a.

Sai dai Ɗan Takarar ya yi watsi da damuwar jama’a game da yanayin sa, yana mai cewa aikin Shugaban ƙasa yana buƙatar ƙarin hankali ne fiye da ƙarfin jiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *