Yadda cinnaka Ya Addabi Dalibai Mata Da Cizo Kafin AGILE Ta Shiga Tsakani

Maryam Abubakar daliba a makarantar sakandire ta GGSSS a karamar hukumar Mashi ta jihar Katsina ta bayyana jin dadinta da sauran daliban makarantar bisa ga samuwar shirin nan na hukumar inganta ilimi da rayuwar yaya mata, AGILE a makarantar ta su.

Maryam ta ce hakika zuwan AGILE ya taimaka masu gaya wajen dakile cizon cinnaka da suke fama da shi a da saboda rashin kujerun zama a cikin azuzuwansu.

” A da ba mu da kujeru sosai a makarantar a kasa muke zama wani lokacin ma cinnaku suna cizonmu, yanzu kuwa mun samu kwanciyar hankali saboda mun samu nutsuwa.” Inji ta.

Dalibar ta ce yanzu suna ganewa sosai a wajen koyarwar da ake ma su.

Maryam Abubakar wacce tana cikin daliban da AGILE ke daukar nauyin karatunsu, ta ce tana amfani da kudin wajen hidimar karatunta.

” Ina sayen littattafai, takalmi, da dinka kayan makaranta. Gaskiya na ji dadi sosai.”

Bayan samar da kujeru da AGILE ta yi a makarantar ta GGSSS Mashi, akwai aikin gyara da gida sabbin azuzuwa da makewayi da ruwa domin samar da kyankyawan yanayi ga dalibai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *