Shirin AGILE Ya Karfafa Man Gwiwa Na Hakura Da Auren Wuri Na Zabi Karatu

Rukayya Abubakar daliba yar kimanin shekaru 16 a makarantar sakandire, Dannakola a karamar hukumar Daura a jihar Katsina, ta bayyana yadda Shirin AGILE ya sanya ta hakura da auren wuri don ci gaba da karatu.

Rukayya ta ce, bayan kammala aji 5 wato SS2 saurayinta ya nemi aurenta tare da sharadin cewa sai ta dai ta hakura da makaranta.

Ta ce, a daidai wannan lokaci ne ta samu tallafin karatu daga hukumar AGILE, bayan samar da azuzuwa da masashe da kuma samar da ruwa da AGILE ta yi a makarantar ta su.

” Dukda iyayena sun kafe kai da fata cewa ya kamata in yi aure amma na fito karara na fada masu cewa dole sai na kammala karatuna kafin na yi aure.” Inji ta.

Ta kuma ce a yayin da saurayin na ta ya ki amincewa da bukatarta sai ta hakura da soyayyar.

Rukayya ta bayyana cewa yanzu haka dai iyayenta sun fahimce ta kuma sun amince ta karasa karatun na ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *