Gwamnan Jihar Katsina Dr Dikko Umar Raɗɗa, ya yadda Kudirinsa na shiga daji don yakar yan ta’adda da ke addabar jihar ta Katsina.
Radda ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da yayi da kafar sadarwar ta BBC hausa kuma suka dora shafinsu na Facebook.
A yayin firar an tabo ma gwamnan bangaren sha’anin tsaro a jihar ya kuma jaddada aniyarsa ta bin sahun jami’an tsaro domin a yaki yan ta’adda da shi.
A bayaninsa ya fadi yadda gwamnatinsa na kirkiro da hanyoyi da take ganin zasu kawo karshen matsalar tsaro.
Daga cikin hanyoyin akwai shirin da ya kaddamar a watan nan na Oktoba na samar da jami’an sintiri guda 1500 tare da raba masu babura 700 da samar da motoci masu sulke guda 10 da kirar Hilux guda 70 ga jami’an tsaron.
In za a iya tunawa dai gwamnan yayi alkawarin shiga daji domin yakar yan ta’adda a jihar a lokacin da yake yakin neman zabe a 2023.
