Gwamnatin Buhari Zata Soke Ƙungiyar ASUU, Ta Yi Rajistar Sabbin Ƙungiyoyi

Gwamnatin Buhari Zata Soke Ƙungiyar ASUU, Ta Yi Rajistar Sabbin Ƙungiyoyi

 

Gwamnatin tarayya ta fara shirin soke rijistar kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato (ASUU).

Rahitanni sun bayyana cewa, kungiyar dake CONUA, ta balle daga ASUU, ta yi rajista a a hukumance a matsayin daya daga cikin kungiyar kwadago.

Wata majiya a Ma’aikatar Kwadago da samar da ayyukan yi ta kasa ta bayyana wa wakilin Dailytrust a ranar Talata cewa, , Ministan Kwadago Chris Ngige, zai gabatar da takardar shaidar rajista ga sabuwar kungiyar kafin safiyar gobe laraba.

Jami’in da ba a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa, matakin da gwamnati ta dauka na daga cikin tsare-tsare na soke rijistar ASUU, da nufin duba yajin aikin da take yi wanda ya hana jami’o’in gwamnati cigaba da karatu na tsawon watanni 7 da suka gabata.

A cewar majiyar, Ministan, a madadin gwamnatin tarayya a yau zai gabatar da takardar shaidar rijista ga kungiyar Congress of Nigerian University Academics (CONUA). Da ta balle daga kungiyar ASUU, wanda ake ganin hakan na iya wargaza kungiyar ta ASUU.

Gidan rediyon Rayhaan ya ruwaito cewa, a watan Satumba ne gwamnati ta yi barazanar janye rajistar kungiyar ASUU a matsayin kungiyar kwadago sakamakon gazawarta na gabatar da rahotannin gudanarwar ta kamar yadda doka ta tanada a cikin shekaru biyar da suka gabata.

A halin da ake ciki kuma, magatakardar kungiyar kwadagon ya rubutawa kungiyar wata tambaya kan dalilin da ya sa ba za a janye shaidar Rajistan ta ba saboda taka doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *