Gwamnatin Tarayya Ta Kai Ƙarar Kamfanin ”Meta”, Ta Nemi Biliyan 30 Kuɗin Tara

Hukumar Kula da Tallace-tallace ta Najeriya ta ce ta kai karar Meta Platforms Incorporated (mamallaka shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp) a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A cewar wata sanarwa a Talatar nan hukumar koli ta kula da harkokin kasuwancin Najeriya, ARCON na neman kanfanin ya biya Najeriya wasu makudan kudade, saboda ci gaba da buga tallace-tallace daban-daban ta hanyar Facebook da Instagram ta amfani da Kamfanin.

A cewar hukumar kamfanin na wannan aiki ne ba tare da tabbatar da an tantance kuma an amince da abubuwan ba, kuma yawancinsu duk sun sabawa ka’ida, kuma hakan haramun ne tare da keta dokar talla a Najeriya.

ARCON ta bayyana cewa Kamfanin na Meta ya ci gaba da yaɗa tallace-tallacen da ba a tantance ba, wanda kuma hakan ya haifar da asarar kudaden shiga ga Gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *