Daga Wakiliyar Mu Amira Salisu Batsari.
Gwamnan Jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin rushe shagunan Kasuwanci Wanda ke kusa da gidan Sanannen Gidan Shugaban Qadiriyya, Malam Nasiru Kabara.
Gwamnan ya bayar da dokar ne, bayan binciken da aka gudanar, inda aka samu cewa Babu wani Izini da masarautar Kano ta bayar dangane da filin wurin.
Manajan Daraktan Hukumar Kula Dokokin Hanya na Jahar Kano (KAROTA) Wanda kuma Shine Shugaban Kwamitin Ruguje Gine-Ginen da basa kan ƙa’ida, Baffa Babba Dan’agundi, ya bayyana cewa, Gwamnatin Jaha ko Masarautar Jahar Kano Babu Wanda ya bada izinin mallakar wannan fili, kamar yadda ake yaɗawa.
Ya bayyana cewa ” Yana da matukar Amfani mutane susan cewa, yin Gina ba bisa ka’ idaba ya haddasa rashin Yarda tsakanin Gwamnatin Jaha da Masarautar jaha da sauran mutane na Bayan lamarin. Bayan Binciken da mukayi, mun gano cewa , Akwai mutanen da kawai sukayi amfani da ra’ayin kansu wajen bada filin wurin.
” A cigaba da Binciken, Gwamna Ganduje ya bada umarni rugeje wurin duka tare da Gina wurin wasannin domin yara, sauran wurin kuma ayi amfani dashi domin Gina wurin zikirin Kadiriyya, wanda za’a katange shi.
Ya ƙara da cewa, Gwamnan ya bayar dokar tura jami’ai a wurin wadanda zasu kasance a wurin Koda yaushe domin bada kariya ga yara, iyaye, a filin wasan daga dukkanin wani wata tarzoma.
