A wannan Alhamis din ne kotun da’ar ma’aikata da ke zaune a Abuja ta bada belin shugaban hukumar karbar korafi da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.
BBC ta ruwaito cewa, belin ya zo ne bisa sharadin bada naira miliyan biyar tare da wasu mutane biyu dukkansu mazauna Abuja da zasu tsaya masa, da kuma nuna shaidarsu ta kwakwkwaran aikin da suke yi.
Hakazalika dole ne sai sun gabatar da hutunansu da na Muhuyi a gaban kotun.
Sannan kuma dole sai shi Muhuyi din ya gabatar da takardar sheda daga wani sannanen mutum mazaunin Abuja dan kasuwa ko kuma mai aikin gwamnati.
