Wani Furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ya maka jarumi Abdallah Amdaz kotu.
Furodusan mai suna Mustapha Ahmad wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe ya maka jarumi Amdaz Kotu ne kan zarginsa da bata masa suna.
Kamar yadda Fim Magazine ta yada akwai kwafin takardar shedar karar ta kotu a cikin labarin.
Shi dai jarumi Abdallah Amdaz ya yi wani barin baki a wajen wani taro da hukumar Hizbah a Kano ta gayyaci yan fim din.
Amdaz ya yi kalaman da suke ganin kamar ya bata ma masu sana’ar suna tare da watsa darajar harkar.
