Ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta soki wani alkali a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Mohammed Umar, kan umarnin da ya bai wa lauya ya durƙusa yayin shari’ar Omoyele Sowore.
Lamarin ya faru ne bayan gardama a kotu tsakanin lauyan Sowore, Marshall Abubakar, da alkalin, lokacin da ake sauraron ƙarar da DSS ta shigar.
NBA ta ce umarnin durƙusawa ba ya cikin hukuncin da doka ta tanada, tana mai jaddada cewa dole ne alkalai su yi amfani da ikonsu cikin iyakar doka da ƙa’idojin shari’a.
Ƙungiyar ta kuma tunatar da lauyoyi da su riƙa nuna ladabi da ƙwarewa a kotu, tare da bin hanyoyin doka wajen bayyana rashin jituwa.
