Wike Ya Ce Har Yanzu Shi Da Mambobin G-5 Basu Cimma Matsaya Da Kowane Ɗan Takara Ba

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya bayyana cewa gwamnonin G-5 ba su cimma matsaya da wani dan takarar shugaban kasa ba gabanin zabe mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a yayin kaddamar da aikin gina titin Eneka-Igbo Etche, a jihar ta Rivers.

G-5 sun hada da Wike, Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), da Samuel Ortom (Benue).

Gwamnonin sun sha fafatawa da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Kungiyar ta dage cewa dole ne Shugaban Jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus.

Sai dai bayan rade-radin cewa kungiyar ta goyi bayan wani dan takara gabanin zaben shugaban kasa a mai zuwa, Wike ya yi watsi da rahotannin, yana mai bayyana su a matsayin ba gaskiya ba ne.

“[Sun ce] Wike ya yi hira da BBC kuma ya ce muna da yunkurin cimma yarjejeniya da dai sauransu. A halin yanzu, babu bidiyo, babu sauti. Wasu kuma daga cikinku suna bata lokacinku wajen sauraron irin wadannan abubuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *