Dukkanin Ƴan Najeriya Sun Amince Da Peter Obi Ya Zama Shugaban Ƙasa – Wani Ɗan Kasuwa
Shahararren dan kasuwa Valentine Ozigbo ya ce Peter Obi da Labour Party (LP) sun samu karbuwa a duk jihohin Najeriya.
Ozigbo ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a bikin cika shekaru 31 da kafuwar Anambra.
Ya kuma ja hankalin al’ummar jihar da su bayar da nasu gudunmuwar wajen ganin an ciyar da siyasa a kasar nan a gaba.
Dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a 2021 ya bayyana fatan cewa zaben 2023 zai haifar da juyin juya hali na cigaba a fagen siyasar Anambra.
