Wasu daga cikin gwamnonin sansanin Nyesom Wike za su marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar baya.
Hakan ya fito ne daga bakin kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku da jam’iyyar PDP Dino Melaye.
Babbar jam’iyyar adawa ta shiga cikin rikici bayan nasarar da Atiku ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa inda ya doke gwamna Wike na jihar Ribas. Tuni dai gwamnan da abokansa suka bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu da ya yi murabus.
Inda suka nuna cewa shi dan yanki daya ne da dan takarar jam’iyyar. Kokarin sulhunta su ya ci tura zuwa yanzu inda Wike da abokansa suka fice daga yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar ta PDP.
Sai dai Melaye, tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya yi imanin cewa wasu daga cikin gwamnonin da ke sansanin Wike za su yi wa jam’iyyar aiki a babban zaben shekara mai zuwa.
“Mene ne aikin Atiku Abubakar a murabus din Ayu ko a’a? Da farko, gwamnonin sun kawo Ayu ne ba tare da izini ko amincewar Atiku ba,” in ji shi a gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Talata.
