Tinubu ya tabbatar wa sojoji inganta jin daɗinsu, ya ce Najeriya ta fara fita daga ƙalubalen tattalin arziƙi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa sojojin Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga inganta jin daɗinsu tare da ci gaba da tallafa wa ayyukan soji na yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga a faɗin ƙasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron buɗa baki na haɗin addinai da ya yi da sojoji da manyan jami’an gwamnati, inda ya yaba wa sadaukarwar da sojoji ke yi wajen kare martaba da ‘yancin kan Najeriya duk da rabuwa da iyalansu da kuma haɗarin da suke fuskanta a bakin aiki.

Shugaban ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar sojoji da iyalansu, yana mai cewa ƙasar za ta ci gaba da gode musu kan jajircewarsu wajen kare ƙasa, musamman a lokacin da ake fuskantar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin ta’addanci da ‘yan bindiga a sassa daban-daban na Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *